Yan sanda sunce suna tsananta farautar barayin mutane.
Rundunar ‘yan Sanda Najeriya ta ce tana farautar mutanen da suka sace mataimakin shugaban wata makarantar Sakandaren Jihar Lagos da daliban su guda 4. Share on Facebook Share on Twitter Senior secondary school students of a school Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Fatai Owoseni ya bayyana haka lokacin da ya ke tabbatar da sace daliban. Wannan ke dada tababtar da sace jama’a dan karbar kudade a Najeriya, ganin ko a farkon wannan mako sanda aka sace wata tsohuwar minista da mai gidan ta a Kaduna. A jiya alhamis dai ne wasu ‘yan bindiga sun sace wani mataimakin shugaban makarantar Model college da wasu dalibai hudu da ke Igbonla a yankin Epe a jihar Lagos. Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Fatai Owoseni ya tabbatar da fkuwar lamarin a lokacin da yake yi wata ganarwa da manema labarai. Mista Owoseni ya ce an gano biyu daga cikin daliban da aka sace. Mun samu wani mummunar labari da ke cewa an sace dalibai hudu da mataimakin shugaban makarantar Model, da ke Epe a safiyar ranar Alhamis. Wadanda suka sace su sun tafi da su a cikin jirgin ruwa. Muna jin labarin muka aike da jami’ai wurin. Mun gano dalibai biyu’. Mista Owoseni ya kara da cewa har yanzu mataimakin shugaban makarantar da dalibai biyu suna hannun wadanda suka sace su. Jami’anmu sun fara nemansu. Muna hada kai dan sojojin ruwa domin nemo su a cikin ruwa dama duk inda suke’, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya rawaito. Matsalar sace-sacen jama’a na kara karuwa a sassan Najeriya daban-daban.
Read more: https://hausa.naij.com/999369-ku-karanta-abinda-hukumar-yan-sanda-na-cewa-kan-masu-yin-garkuwa-da-mutane-a-jihar-legas.html